Tarihin Mohammed Morsi yana cewa ‘Ni aka zalunta’

Mohammed Morsi


Morsi ne zababben shugaban kasar Masar na farko

Mohammed Morsi shi ne zababben shugaban kasar Masar na farko, wanda sojoji suka hambarar bayan shekara daya kawai a kan mulkin a ranar 3 ga watan Yulin 2013.

Yunkurin sojojin ya biyo bayan zanga-zangar da ‘yan kasar suka shafe kwanaki suna yi da kuma bijire wa umarni sojojin da ya yi na ya kawo karshen halin da siyasar kasar ta shiga a lokacin bayan tumbuke Hosni Mubarak a shekarar 2011.

Wata hudu bayan hambarar da shi aka gurfanar da shi a gaban kotu tare da sauran mutum 14 na kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood, inda aka zarge su da iza magoya bayansu wajen kisan masu zanga-zanga.

Haka zalika an kuma zarge su da tsarewa tare da azabtar da wasu daga cikin masu zanga-zangar.


Morsi ya mutu yana da shekara 67

Zarge-zargen sun danganci gwabzawa da aka yi tsakanin magoya bayan ‘yan adawa da kuma magoya bayan jam’iyyar Brotherhood a wajen fadar shugaban kasa ta Ittihadiya da ke Alkahira a 2012.

A zaman kotun na farko, Morsi ya daga murya daga cikin kejin da ake tsare da shi a cikin kotu yana mai cewa shi “Ni aka zalunta da juyin mulki” sannan kuma ya yi watsi da ikon kotun na shari’ar da take yi masa.

An wanke shi daga zargin kisan kai amma an daure shi shekara 20 bisa umarnin da ya bayar wajen tsarewa da kuma azabtar da masu zanga-zanga.

Daga baya kuma aka yanke masa hukuncin kisa bayan tuhumarsa da wasu karin laifukan, kafin daga bisani a janye hukuncin.

Ya rasu ne yayin da ake tsaka da yi masa shari’a a harabar kotu ranar 17 ga watan Yunin 2019.

Dan majalisar ‘Yanuwa Musulmi

Karan Morsi ya kai tsaiko a kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi bayan ya zama dan majalisar kasa a matsayin Indifenda daga shekara ta 2000 zuwa 2005.

A matsayin dan majalisa, an sha yabonsa kan yadda yake da fasahar iya zance, kamar yadda ya yi a 2002 lokacin da aka samu hatsarin jirgin kasa, inda ya soki gazawar gwamnati.

An zabe shi a matsayin dan takarar jam’iyyar ‘Yan’uwa Musulmi a watan Afrilun 2012 bayan mataimakin shugaban jam’iyyar kuma hamshakin dan kasuwa Khairat al-Shater ya ajiye aikinsa.

A yayin kamfe dinsa, Morsi ya gabatar da kansa a matsayin wani bango da zai dakile duk wani yunkuri na dawo da salon tsohuwar gwamnatin Hosni Mubarak.


An yanke wa Morsi hukuncin kisa wanda aka janye daga baya

Sojoji sun gargadi Morsi cewa za su shiga cikin rikicin matukar bai gamsar da ‘yan kasa ba, kuma suka ba shi kwana biyu a matsayin wa’adi.

A yammacin 3 ga watan Yuli, sojoji suka dakatar da kundin tsarin mulkin kasar sannan suka sanar da kafa wata kwarya-kwaryar gwamnatin kwararru ta wucin-gadi kafin sabon zabe.

Morsi ya yi Allah-wadai da wannan yunkuri a matsayin juyin mulki.

Shugaban sojin kasar, wanda shi ne shugaban kasar a yanzu Abdul Fattah al-Sisi, shi ne ya ba da umarnin kama shi.

Sojoji sun tafi da shi zuwa wani boyayyen wuri, inda aka shafe mako biyu ba tare da jin duriyarsa.

An haifi Morsi ne a kauyen El-Adwah a gabar kogin Nilu a lardin Sharqiya a shekarar 1951.

Ya yi karatu a fannin injiniya a Jami’ar birnin Alkahira a shekarun 1970 kafin ya tafi kasar Amurka, inda ya kammala digiri na uku a can.

Bayan da ya samu nasara a zaben 2012, ya yi alkawarin cewa “gwamnatinsa za ta tafi da duka ‘yan Masar”.

Sai dai masu suka sun ce gwamnatinsa ta kasa cirewa ‘yan kasar kitse a wuta.

An yi zarginsa da barin masu tsananin kishin addinin Islama cin karensu babu babbaka a fagen siyasar kasar da rashin iya tafiyar da tattalin arzikin kasar.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...