Taraba: An saka dokar hana fita a garin Takum

An saka dokar hana fita a garin Takum dake jihar Taraba bayan da rikicin da ya barke tsakanin yan kabilar Tiv da Jukun ya shiga rana ta biyu.

Binciken da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa Jukunawa ne suka je kai harin ramuwar gayyar kisan wani mutum dan kabilar su da ake zargin yan kabilar Tiv da aikatawa.

Yan kabilar Tiv da dama aka kashe tare da kona gidaje ya yin harin na ramuwar gayya abin da ya tilastawa da yawa daga cikinsu tserewa daga garin.

Wani mazaunin garin ya fadawa jaridar ta Daily Trust cewa yanzu an samu kwanciyar hankali a garin kuma kowa na cikin gidajensu ya yin da sojoji ke cigaba da sintiri akan tituna.

Amma kuma mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Taraba DSP David Misal ya ce mutum daya kaÉ—ai aka kashe kuma tuni aka shawo kan lamarin.

Garin Takum nan ne mahaifar Janaral TY Danjuma mai ritaya da kuma gwamnan jihar Darius Ishaku, ya kums dade yana fama da rikici da kuma matsalar garkuwa da mutane.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...