Tanzania: Matsafa sun yanke sassan jikin wasu yara

Map showing Tanzania

Hukumomi a kasar Tanzania sun bayyana cewa an hallaka yara shida a kudu maso yammacin kasar sannan aka cire kunnuwa da hakoransu.

Kazalika an gano cewa an cire yatsun yaran, wadanda shekarunsu suka kama da shida zuwa tara.

Kwamishiniyar lardin Njombe Ruth Msafiri ta ce “An yi hakan ne domin yin tsafi da sassan jikin nasu kuma wasu na ganin za su zama attajirai idan suka yi tsafi da sassan jiki.”

‘Yan sandan sun tsare wani mutumwanda dan uwa ne ga uku daga cikin yaran, bisa zargi da hannu a kisan su.

Yara goma ne suka bata a lardin Njombe tun farkon watan Disamba ko da yake an gano hudu da ransu.

Wakilan BBC sun ce matsafa ne suke sanya wa a kashe yara sannan a vcire wasu sassan jikinsu domin yin asirin da wasu ke gani zai sa su zama attajirai.

Kwamishiniyar ta shaida wa BBC cewa “Muna kira ga iyaye da su sanya ido sosai kan yaransu sannan su rika gaya musu inda za su idan sun fita.”

An sace yaran ne daga gidajensu da tsakar dare lokacin iyayensu sun tafi kasuwa inda suke kasuwanci.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

‘Makwabcina ne ya guntule hannuna’ (Daga Tanzania a 2017)

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...