Sudan: Malaman jami’a sun fara zanga-zanga

Men in a pickup truck

Hakkin mallakar hoto
Protester

Jami’an tsaro a Sudan suna tsare da wasu malaman jami’a da suka fito zanga-zanga a Khartoum, babban birnin kasar.

Likitoci da dama sun fito suna zanga-zanga a asibitoci inda suke kira da shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa, kuma tun watan Disambar bara jama’ar kasar ke karawa da jami’an tsaro.

Kungiyar Human Rights Watch mai fafutukar kare hakkin bil Adama ta ce jami’an tsaro sun kashe akalla mutum 50.

Ba kamar yadda aka saba gani a wasu sassa na nahiyar Afirka ba – inda yawancin masu fita zanga-zangar adawa da gwamnati kan kasance matasa marasa aikin yi ne.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Omar al-Bashir ya mulki Sudan tun 1989

Amma a Sudan likitoci maza da mata da malaman makaranta da sauran ma’aikata ne ke fuskantar harsasai da hayaki mai sa hawaye da kuma kulakan ‘yan sandan gwamnatin Shugaba Omar al Bashir.

‘Yan sa’o’i kadan da suka gabata an kame wasu malaman jami’a a birnin Khartoum.

An kuma gabatar da wasu jerin zanga-zanga a asibitoci goma cikin babban birnin kasar – an kuma bukaci Shugaba Omar al Bashir ya sauka daga mukaminsa.

Mako biyu da ya gabata gwamnatin Sudan ta ce za ta saki dukkan wadanda ta damke sakamakon zanga-zangar da aka shafe fiye da wata biyu ana yi a fadin kasar.

Amma yawancin wadanda ke tsaren ba su sami ‘yancinsu ba.

Masu rajin kare hakkin dan Adam a Sudan na fargabar cewa gwamnati na iya kama su domin gwamnatin kasar na tsare da mutane masu yawa a wurare na sirri.

Suna kuma tsorn jami’an tsaron na iya gallaza masu azaba.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...