Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin samar da tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar bindiga da ake nema ruwa a jallo.
Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce an kama wanda ake zargin a bisa zargin dake cewa yana da hannu a harin da aka kai na jajiberin Kirismeti a wani bangare na ƙauyukan ƙananan hukumomin Ɓokkos da Barikin Ladi.
Sama da mutane 115 aka tabbatar sun mutu a wani hari da ƴan bindiga suka kai a ƙauyukan dake ƙananan hukumomin biyu.
Makama ya ce sojojin sun kama wanda ake zargi a ranar 4 ga watan Yuni a unguwar Furata dake yankin Lamingo a Jos.
Kan