Sojojin sun kama wani mai safarar bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin  samar da  tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar  bindiga da ake nema ruwa a jallo.

Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce an kama wanda ake zargin a bisa zargin dake cewa yana da hannu a harin da aka kai na jajiberin Kirismeti a wani bangare na ƙauyukan ƙananan hukumomin Ɓokkos da Barikin Ladi.

Sama da mutane 115 aka tabbatar sun mutu a wani hari da ƴan bindiga suka kai a ƙauyukan dake ƙananan hukumomin biyu.

Makama ya ce sojojin sun kama wanda ake zargi a ranar 4 ga watan Yuni a unguwar Furata  dake yankin  Lamingo a Jos.

Kan

More from this stream

Recomended