Sojojin Najeriya sun yi mummunar ta’asa wa ƴan bindiga a Kaduna

Dakarun Sojojin Najeriya sun yi nasarar halaka ‘yan bindiga shida da ke addabar mazauna karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Laftanar Kanar Musa Yahaya, ya ce ‘yan bindigar sun haɗu da ajalin nasu ne a ranar Alhamis lokacin da sojojin da ke aiki da sahihan bayanan sirri suka kai wani samame a kauyukansu a Sabon Birnin, Dogon Dawa, Saulwa, Maidaro- Ngede Allah da Kidenda duk a karamar hukumar Birnin-Gwari.

Ya bayyana cewa sojojin sun taɓo ‘yan ta’addan inda nan take suka yi artabu da su har suka kashe shida daga cikinsu.

Sojojin, a cewar kakakin rundunar, sun kuma kwato bindigogin AK-47 guda biyu, da gidan albirushin AK-47 guda hudu, harsashi guda goma sha hudu na 7.62mm, rigunan ‘yan fashi guda arba’in, da kuma babura tara.

More News

Dakarun Najeriya sun cafke wasu ƴan’aiken ƴanbindiga a Kaduna

Sojoji sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da kaiwa 'yan bindiga sakonninsu a kasuwar ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia a...

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴanbanga sun sake kawar da wani ƙasurgumin ɗanbindiga

Rahotanni da ke fitowa daga Arewa maso Yammacin Najeriya na nuna cewa an yi nasarar kawar da wani fitaccen dan bindiga a jihar Zamfara,...

Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan...