Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ‘yan ta’adda 37 da ‘yan fashi 12

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai ta sojojin Najeriya sun kashe mutanen da suka kira ‘yan ta’adda 37 a yankin arewa maso gabashin ƙasar tare da kama wasu 17 cikin mako biyu da suka wuce.

Kazalika, dakarun sun kashe ‘yan fashin daji 12 sannan sun kama 15 tare da ƙwace makamai 21 da ƙunshin harsasai 117 iri daban-daban, ciki har da mota mai bindiga huɗu daga hannun mutanen.

Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Benard Onyeuko, shi ne ya bayyana hakan yayin jawabinsa game da ayyukan rundunar a mako biyu da suka wuce a Abuja ranar Alhamis.

Ya ce sun yi nasarar ceto mutum 16 da aka yi garkuwa da su, yayin da “ƴan ta’adda” 863 da iyalansu suka miƙa wuya.

“Dakarunmu sun ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji da sauran miyagu a dukkan sansanoni da ke faɗin ƙasa cikin mako biyu da suka wuce, inda muka samu kyakkyawan sakamako,” in ji shi.

More from this stream

Recomended