Connect with us

Hausa

Sojoji ‘sun tursasa wa wasu ‘yan Kenya iyo a ruwan ba-haya’

Published

on

Ruwan kwata

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu ‘yan kasar Kenya sun shiga shafin Twitter don bayyana fushinsu kan wani rahoton da wata jaridar kasar, Standard Newspaper, ta wallafa cewa wasu sojoji sun ci zarafin wasu mazauna birnin Mombasa da ke bakin ruwa, a ranar Lahadi a lokacin da ake bukukuwan ranar gwarzaye.

An tsaurara matakan tsaro a birnin, a yayin da kasar ke bukukuwan wanda shugaban kasar, Uhuru Kenyatta, da wasu manyan kusoshin gwamnati suka halarta.

Jaridar ta wallafa rahoton da ke cewa an tursasa wa wasu mazauna birnin yin ninkaya a cikin ruwan ba-haya, yayin da kuma aka tursasa wa wasu zama a cikin tabo.

Wasu kuwa mazauna yankin sun yi zamansu ne a gida, saboda tsoron ka da sojoji su muzantasu, a cewar rahoton.

Sai dai kawo yanzu sojojin ba su ce komai ba game da zarge-zargen.

Wani matashi mai shekara 23 a duniya wanda ake kira Chikore, ya shaida wa jaridar cewa, yana kan hanyarsa ce ta zuwa wajen taron bikin lokacin da sojoji suka tsayar da shi saboda basu yarda da shi ba.

“Sun yi kokawa da ni har suka kaini kasa, daga nan kuma suka sa na yi iyo a cikin ruwan ba-haya. Na yi kokarin gudu amma sai suka buga mini gindin bindiga,” In ji shi.

Masu mu’amala da shafin Twitter sun bayyana wannan lamarin da cewa “abin kunya ne” kuma “abin kyama”:

Facebook Comments

Hausa

Kasashen Nijer Da Benin Za Su Gana Da Najeriya Akan Sake bude Iyakokinta

Published

on

A yayinda kasashen Nijer, Benin da Najeriya ke shirin tattauna hanyoyin sake bude iyakokin Najeriya a yau Alhamis, 14 ga watan Novemba, a Abuja babban Birnin Tarayyar Najeriya, gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta sanar cewa, matakin na hukumomin Najeriya ya haddasa gibin dubban miliyoyin CFA a asusunta sakamakon tauyewar al’amura akan iyakokin kasashen biyu.

Da yake ganawa da wata tawagar jami’an asusun bada lamuni na FMI ko IMF a ranar talatar da ta gabata, ministan kudaden kasar Nijer Mamadou Diop ya sanar cewa, matakin rufe iyakokin Najeriya ya haifar da gibi a aljihun gwamnati, a cewar sa asarar billion 40 na CFA ne wannan mataki ya janyowa kasar Nijer saboda rashin samun kudaden da aka yi hasashen zasu shiga aljihun gwamnati ta hanyar awon kaya da biyan wasu diyyoyin kan iyakar kasar da Najeriya.

Ministan kudin kasar ta Nijer ya kara da cewa tuni ma’aikatan harkokin kudade suka bullo da wasu sabbin matakai don cike wannan gibi, kafin karshen shekara yayinda a dayan gefe wasu abokan hulda suka amince zasu tallafa da gudunmowar warware wannan matsala injishi.

Dr. Soly Abdoulaye masanin tattalin arziki a Nijer ya ce, faruwar wannan al’amari wani abu ne da ya kamata ya zamewa gwamnatocin Afrika irinsu Nijer darasi.

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijer Kalla Hankourao a karshen taron kungiyar CEDEAO da aka gudanar a makon jiya a Yamai, ya bayyana cewa kasashen Nijer da Najeriya da Benin zasu gudanar da taro a Abuja babban Birnin Tarayyar Najeriya, domin duba hanyoyin sassauta wannan mataki da ya jefa miliyoyin talakawa cikin halin kuncin rayuwa.

Ga cikakken rahoton Wakilin muryar Amurka a yamai Souley Moumouni Barma.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

APCn Jihar Edo ta dakatar da Adams Oshiomole

Published

on

Oshiomole

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Oshiomole bai ce komai ba game da dakatarwar

Jam’iyyar APC reshen jihar Edo ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Comrade Adams Oshiomole.

Shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 18 a jihar ne suka kada kuri’ar yanke kauna kan Adams Oshiomole a ranar Talata, kamar yadda shugaban jam’iyyar na jihar Aslem Ojezu ya shaida wa manema labarai.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamna Oshiomole da kuma mai-ci Godwin Obaseki suna kokawar neman iko ne da jam’iyyar a jihar ta Edo.

Sai dai Oshiomole bai ce komai ba game da dakatarwar, sannan kuma babu tabbas kan yadda hakan zai shafi aikace-aikacensa a matakin kasa a matsayinsa na shugabanta.

Rikicin ya samo asali ne tun daga watan Yuni lokacin da ‘yan majalisa tara cikin 24 na majalisar jihar suka zabi kakakin majalisar da sauran shugabanninta.

Za mu ci gaba da bin wannan labari domin kawo maku karin bayani da zarar mun samu.

Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

An dakatar da ma’aikatan gwamnati 500 a jihar Adamawa

Published

on

Fintiri

Gwamnatin jihar Adamawa ta dakatar da wasu ma`aikatan Kwalejin fasahar jihar kusan mutum 500 daga aiki.

Gwamnatin dai ta ce ta sallame su ne saboda ba a bi ka`ida ba wajen daukarsu aiki.

Hakan na zuwa ne bayan da wani kwamitin da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya kafa ya gudanar da bincike, wanda a cikin rahotonsa ya gano kura-kurai a daukar da aka yi wa ma`aikatan.

To sai dai ma’aikatan da aka dakatar sun musanta batun rashin cika ka’ida wajen daukar tasu.

Wata malamar kwalejin da sallamar ta shafa ta ce rayuwarta ta gigita tun bayan dakatarwar.

“Na karbi takardar nan, ina fita ban san inda kaina yake ba kawai sai na fadi. Duniyar gaba daya ta fita daga kaina ban san mene ne yake yi min dadi ba.

“Wata bakwai ina aiki ba a biya na. Kuma an tantance ni, ba ni da wata matsala. Iyayena ba su da karfi sannan ga marayu a gabana.”

Gwamnatin dai ta yi zargin cewa wasu ma`aikatan ba su da cikakkiyar shaidar kammala karatu ko kwarewa, yayin da wasu kuma take zargin gwamnatin da ta gada ce ta gaggauta daukarsu aiki a lokacin da wa`adinta ke gab da cika.

Sai dai wasu daga cikin ma`aikatan da aka sallama, sun ce babu gaskiya a hanzarin da gwamnatin ke kawowa.

Hasali ma dakatarwar ta shafi wasu ma`aikatan da ke wasu ma`aikatun gwamnati.

Sai dai gwamnatin jihar Adamawa a nata bangaren, ta ce har yanzu ba ta yanke shawara a kan makomar sauran ma`aikatan da ba na kwalejin fasahar ba, wadanda aka dakatar da su, kasancewar kawo yanzu ba a mika mata cikakken rahoto a kan su ba.

Gwamna Ahmadu Fintiri dai ya yi ikirarin kyautata rayuwar ma`aikata tun lokacin yakin neman zabe, abin da ke daure kai shi ne yadda gwamnatinsa ta fara sa kafar-wando guda da irin wadannan ma`aikata.

To sai dai da ma tun a lokacin da yake kaddamar da gwamnatinsa ya ce ba zai iya tafiya da ma`ikatan da gwamnatin da ya gada ta dauka aiki tana gab da shudewa ba.

Facebook Comments
Continue Reading

Trending

© Copyright 2019 - AREWANG Media Limited