Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram da mayakan ISWAP a Yobe

Rundunar sojin Najeriya ta ce a ci gaba da yaki da take da ” ‘yan ta’adda” a yankin arewa maso yammacin Najeriya, dakarun bataliya ta 120 da hadin gwiwar JTF sun kashe yan Boko Haram da mayakan ISWAP masu yawa da safiyar yau, a wani harin kwantan bauna da suka yi musu a kauyen Ngirbua da ke jihar Yobe.

A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafukanta na sa da zumunta, rundunar ta ce dakarunta sun kashe mayaka da dama tare da kwace makamansu, amma sauran bayani kan abin da ya faru zai zo daga baya.

More from this stream

Recomended