Sojoji sun kashe yan bindiga da dama a Kaduna

0

Jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara a yakin da suke da yan bindiga bayan da sojojin kasa da na sama suka kashe Yan bindiga da dama a wani farmaki da suka kai a yankin Galbi dake karamar hukumar Chikun ta jihare Kaduna.

Kwamishinan tsaro na jihar Kaduna,Samuel Aruwan shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

A cewar sanarwar jami’an rundunar Operation Forest Sanity da hadin gwiwar sojojin sama sune suka kai farmaki a matartarar yan bindigar dake yankin na Galbi.

Aruwan ya bayyana cewa a yayin farmakin sai da sojojin suka tsallaka kogin Kaduna inda suka fuskanci turjiya daga yan bindigar.

Bayan dauki ba dadi ne sojoji sun samu nasarar kashe yan bindiga masu yawa tare da samun bindigogi kirar GPMG guda biyu, AK47 guda uku sai kuma baburan hawa guda bakwai.