Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram Alhaji Modu da wasu mayaka 27

0

Dakarun rundunar sojan Najeriya dake yaki da yan ta’addan Boko Haram a yankin arewa maso gabas sun kashe Alhaji Modu daya daga cikin gawurtaccen mayakan Boko Haram.

A cewar Zagazola Makama wani masani kan yaki da yan ta’adda ya ce Modu wanda aka fi sani da Bem Bem an kashe shi tare da wasu mayakan kungiyar su 27.

Ya ce an kashe Modu ne ranar 3 ga watan Agusta a wani harin sojan sama a tsaunukan Mandara dake ƙaramar hukumar Gwoza.

A cewarsa bayanan sirrin da rundunar ta samu sun bayyana cewa mayakan na kungiyar ISWAP suna tattaruwa a yankin domin kai hari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here