Sojoji sun kama wani soja da ya yi yunkurin Safar harsashi daga Maiduguri

Dakarun rundunar sojan Najeriya shiya ta 7 dake Maiduguri sun kama wani sojan mai suna Nathaniel Jerimiah ɗauke da harsashi a cikin kayansa a tashar motar Borno Express dake Maiduguri.

Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi ya ce an bawa Jerimiah hutu ne kuma yana kan hanyarsa ne ta zuwa Adamawa lokacin da a aka kama shi.

Dakarun sun gano harsashi 89 a ɓoye a cikin jakarsa lokacin da su ke gudanar da bincike.

Makama ya ce an gaggauta tsare sojan domin yi masa tambayoyi a yayin da aka miƙa harsashin ga hukumomin da abin ya shafa domin cigaba da bincike.

Kawo yanzu daraktan yaɗa labarai na ƙaramar rundunar sojan Najeriya, Onyeama Okechukwu bai ce komai game batun.

More from this stream

Recomended