Sojoji Sun Kama Mayaƙan Boko Haram Biyu

Sojojin rundunar Operation Hadin Kai dake yaki da yan ta’adda a yankin arewa maso gabas sun samu nasarar kama wasu mayakan Boko Haram biyu.

Mayakan na Boko Haram sun fada hannun jami’an tsaron ne biyo bayan musayar wutar da aka gwabza tsakanin dakarun sojan da yan ta’addar a wajen kauyen Tumballa dake dake kusa da karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

A wani labarin kuma wasu mayakan na Boko Haram biyu sun mutu bayan da nakiyar da suke shirin danawa a hanyar da sojoji suke sintiri ta tashi da su a ranar Lahadi 31 ga watan Disamba.

Bam din da suke ɗanawa ya tashi da su tare da yi musu gunduwa-gunduwa a kauyen Genderi dake kan iyakar Kamaru a yankin tafkin Chadi.

More from this stream

Recomended