Sojoji sun kama jiragen da ake satar mai da su a yankin Niger Delta

Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya, ta sanar cewa ta Kama wasu jiragen ruwa goma sha biyu, da ke dakon mai da aka sato a yankin Neja Dalta, a wani samamen hadin gwiwa da ta kaddamar a yankin mai suna Operation Dakatar da Barawo.

Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya, Commodore Ayo Adedatun, ya ce rundunar ta kaddamar da wannan aiki na musamman na yakar masu satar danyen mai a yakin na Neja Delta ne da hadin gwiwar babban Kamfanin Man Najeriya, NNPC. An kaddamar da shirin ne a watan Afirilu na wannan shekarar, kuma an samu gagarumar nasara wajen kama barayin mai da kuma wasu jiragen ruwa tara na dakon man da aka sato.

Ya a kuma kama wasu barayi a Fatakwal da Yanagua na jahar Bayelsa da Worri. An kuma kama wani man da aka sato daga yankin tsibirin Bonny na jahar Rivers. Rundunar ta ce matasan yankin na dada zama babbar matsala gare ta. Yace daya daga cikin kalubalen da su ke fuskanta shi ne rashin samun hadin kai daga matasa, da kungiyoyin sa kai da kuma sauran al’ummomin yankin.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...