Sojoji sun harbe yan bindiga 4 a Kaduna

0

Rundunar tsaron soja ta Operation Forest Sanity ta samu nasarar harbe wasu yan bindiga hudu a maboyarsu dake Tsohon Gayan a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce sojojin sun kuma samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, harsashi 22 da kuma babur guda daya.