Sojoji Sun Ceto Mata Da Yara 10 Bayan Da Suka Shafe Kwanaki 44 A Hannun Ƴan Fashin Daji

Gwamnatin jihar Katsina ta ce mata 10 ne da kuma ƙananan yara tara aka ceto daga cikin mutanen da ƴan fashin daji suka yi garkuwa da su watan da ya wuce.

Gwamnatin ta ce dakarun rundunar sojan Najeriya ne suka samu nasarar ceto mutanen.

A ranar 3 ga watan Faburairu mutane 55 ne aka yi garkuwa da su lokacin da suke kan hanyar raka wata amarya dakinta zuwa garin Damari a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar.

Ƴan kwanakin  da suka wuce wani fefan bidiyo ya karaɗe kafafen soshiyal midiya inda masu garkuwar suka yi barazanar aurar da amarya matukar ba a fanshe ta ba.

A wata sanarwa ranar Litinin, Ibrahim Kaulaha mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina,ya ce waɗanda aka ceton an miƙa su ga hannun shugaban ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar.

Mohammed ya ce Dikko Radda ya yabawa sojojin kan bajinta da suka nuna wajen aikin ceto mutanen

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...