Dakarun sojan sama na rundunar samar da tsaro ta Operation Whirl Punch sun kashe yan fashin daji masu garkuwa da mutane da basu gaza 30 ba a wani harin sama da suka kai a wajejen Kwiga zuwa Kamfanin Doka dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojan saman Najeriya, AVM Edward Gabkwet ya sanar ranar Litinin a Abuja.
Gabkwet ya ce an kai harin ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu na ganin gungun wasu yan bindiga a yankin.
Ya ce bayanan sirrin da aka samu ya nuna cewa yan ta’addar sune dai suka kai wa sojoji harin kwanton ɓauna a Kwanar Mutuwa ranar 27 ga watan Janairu da kuma wasu hare-hare da kuma garkuwa da mutanen da basu ji basu gani ba a Birnin Gwari.