Shugabannin Addinai Na Zargin Juna A Kan Batun Satar Mutane A Kaduna

Sakataren majalisar limamai da malamai na jihar Kaduna, Malam Yusuf Yukub Arrigasiyyu ne ya yiwa manema labarai bayani kan taron gaggawa da majalisar ta kira a garin Kaduna.

Arrigasiyyu ya ce kalaman shugaban kungiyar kiristocin za su iya haddasa da rashin fahimta tsakanin mabiya addinai a jihar Kaduna idan ba a dauki mataki ba.

Shima limamin anguwan Rimi, Imam Musa Tanimu wanda ya yi magana da yawun limamai kuma ya nuna damuwa yana mai cewa an kama Musulmi da limamai da dama amma basu taba jingina wannan matsala a kan addini ba.

To sai dai shugaban kungiyar kiristoci ta jihar Kaduna Reveran Joseph John Hayap ya ce daukar nauyin kungiyar limamai aka yi shi ya sa su ka jirkita ma’anar bayanin da ya yi game da hauhawar sace-sace a jihar Kaduna.

Rev. ya ce ba inda ya ce kiristoci kawai ake sacewa a jawabin shi amma dai tun da shi shugaba ne dole ya kare muradin mabiyan shi saboda ya ce har gida ake bi ana sace kiristoci a Kaduna ba sai sun fita kan hanya ba.

Duk da bayanan kokarin kawo karshen sace-sacen mutane da gwamnatoci ke yi a Arewachin Nigeriya dai har yanzu ana ci gaba da samun rahotannin dauki dai-dai a wasu sassan wannan kasa.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...