Shugaba Buhari na bukatar Kafa Kotunan Musamman

(VOA Hausa)

Wannan a cewar shugaba Buhari, zai taimaka ainun wajen magance matsalar tsaiko da ake samu a shari’o’in cin hanci da rashawa a kotunan kasar.

Buhari ya yi wannan kiran ne sa’adda ya bude wani taron kasa na kwanaki biyu a kan yaki da cin hanci da rashawa a aikin gwamnatin, wanda hukumar yaki da ayyukan cin hanci da rashawa ta ICPC, tare da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya suka shirya a fadar gwamnatin da ke Abuja.

Ya ce kafa kotuna na musamman na shari’o’in cin hanci da rashawa, zai baiwa gwamnatin damar cimma burin ta na ganin an kwato dukiyoyi na haram da kadarorin da aka mallaka ba bisa ka’ida ba, da kuma uwa uba, hukunta wadanda aka kama da aikata irin wadannan laifuka.

Shugaban kasar yayi amfani da damar taron inda ya bayyana irin illoli da matsalar cin hanci da rashawa ya ke haifarwa ga tattalin arzikin Najeriya da rayuwar al’ummar ta.

Da ya ke karin haske a kan jawabin shugaban kasa a wurin taron, Kakakin Fadar Shugaban Kasa Garba Shehu, ya ce “akwai damuwa a bangaren gwamnatin da hukumar ICPC, yadda ake daukar tsawon lokaci kafin a yanke hukunci a shari’un da suka shafi cin hanci da rashawa a kotunan yau da kullum”.

Garba Shehu ya ce wannan yanayin yana shafar kudurorin gwamnatin na inganta sha’anin ilimi da yaki da ta’addanci da kalubalen tsaro da ya addabi yankuna da dama na kasar.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...