Shin me ya sa aka fitar da Madrid daga Zakarun Turai?

Real Madrid

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mulkin Real Madrid a Turai ya kawo karshe bayan ta sha kashi har gida a hannun Ajax a gasar Zakarun Turai ta Cha,mpions Leage, gasar da kungiyar ta mamaye tun 2016.

Cikin mako daya an rusa wa Real Madrid burin lashe kofuna a kakar 2018/2019 bayan Barcelona ta fitar da ita daga gasar Copa del Rey kuma ta kara ba ta tazara a La liga kafin Ajax ta fitar da ita daga gasar Zakarun Turai a Bernabeu.

Real ta lashe kofin gasar zakarun Turai sau uku a jere, sau hudu kuma cikin shekara biyar.

Karon farko da Real Madrid ta gaza tsallakewa zuwa zagayen dab da kusa da karshe tun 2010.

Akwai wasu dalilai da ake ganin suka janyo wa Real Madrid shiga wannan halin, kuma sun hada da:

Shekarun‘Yan wasa

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ana ganin Gareth Bale da Benzema sun kai karshen ganiyarsu a Madrid, duk da Benzema yana kokarin cin kwallaye bayan tafiyar Ronaldo.

‘Yan wasa kamar Luka Modric da Isco da Marcelo ba su taka rawar da suka saba takawa ba kamar a shekarun baya da suka taimaka wa Real Madrid lashe kofin Zakarun Turai sau uku a jere.

Shekarun manyan ‘yan wasan ya yi tasiri, kamar Luka Modric shekararsa 33, Sergio Ramos shekara 32, Toni Kroos shekara 29 yayin da kuma Karim Benzema ke da shekara 31.

Ana ganin tauraruwar Isco da Marcelo ta disashe sabanin baya, duk da cewa ‘yan wasan na ikirarin cewa babu wani abin da ya sauya.

Amma wani zai ce ko me ya sa Real Madrid take fadi-tashi a kakar bana?

Sannan babu wani babban dan wasa masanin raga da zai iya farfado da kwazo da karfin Madrid na cin kwallaye.

Wasu dai na ganin Real Madrid na bukatar zubin sabbin ‘yan wasa domin farfado da martabar kungiyar.

Babu Ronaldo

Yadda aka fitar da Real Madrid tun a zagayen ‘yan 16 a Zakarun Turai ya nuna kungiyar ba ta iya lashe kofin sai da Ronaldo.

Wannan ce kuma Shekarar farko da Real Madrid ta fara rayuwa ba Ronaldo, bayan ya koma taka leda a Juventus a kakar da ta gabata.

Karon farko kenan tun 2015 da aka fitar da Real Madrid a gasar Zakarun Turai.

Masharhanta da dama na ganin rashin Ronaldo ya yi tasiri sosai ga rashin nasarorin da Madrid ke fuskanta a kakar bana. Tun daga fatarar cin kwallaye zuwa ga nasarar lashe wasanni.

Kuma har yanzu Real Madrid ta gaza maye gurbinsa da wani fitaccen dan wasa.

A bana Benzema ne dan wasan da ya fi ci wa Real Madrid kwallaye a raga a gasar Zakarun Turai inda ya ci hudu, kuma yake bayan Robert Lewandowski na Bayern Munich da ke da kwallaye takwas da kuma Lionel Messi da ke da kwallaye shida.

Rashin Ramos

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sergio Ramos na da matukar muhimmanci a Real Madrid kamar Cristiano Ronaldo.

Ajax ta lallasa Real Madrid ne ba tare da Ramos ba bayan ya karbi katin gargadi na biyu a karawa ta farko a Netherlands.

Ramos ya ci wa Real Madrid kwallaye biyu masu muhimmanci a wasan karshe a gasar Zakarun Turai.

Ramos ne babban mai tsaron bayan Real Madrid, kuma wasu na ganin komi na iya faruwa da Madrid saboda rashinsa.

Ajax ta samu damar yayyaga bayan Real Madrid ne saboda rashin Ramos.

Sauyin Koci

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Solari ya sha kashi a sau hudu a wasanni biyar

Tun tafiyar Zineden Zidane abubuwa suka dagule wa Real Madrid.

Zidane ne ya kafa lashe wa Real Madrid kofin zakarun Turai sau uku a jere, tarihin da babu wani koci da ya taba kafawa a Turai.

A karshen kakar 2017/2018 ne Zidane ya ajiye aikinsa na horar da ‘yan wasan Real Madrid, watanni 10 kuma yanzu bayan tafiyarsa abubuwa sun sauya wa kungiyar.

Sauye-sauyen koci a kaka daya wasu na ganin shi ne ya jefa Real Madrid cikin halin da take ciki a yanzu.

A watan Nuwamba ne Santiago Solari ya karbi aikin horar da Real Madrid bayan korar Julen Lopetegui.

Duk da Solari ya yi nasara a wasanninsa na farko, amma yadda babbar abokiyar hamayya Barcelona ta bi Real Madrid har gida Santiago Bernabeu ta doke ta a Copa del Ray da La Liga ya nuna ba zai iya ba.

Solari ya sha kashi sau hudu a wasanni biyar da ya buga na baya-bayan nan.

Kocin dai ya ci gaba da tafiyar da Real Madrid tare da zubin ‘yan wasan da ya gada ba tare wani sabon zubi ba.

Ko da yake wasu na ganin ya yi kokari yadda ya tada matasan ‘yan wasa kamar Vinicius Junior da ake ganin zai gaji Ronaldo da kuma wasu matasa kamar Alvaro Odriozola da Sergio Reguilon da Dani Ceballos da kuma Marcos Llorente.

Wasu na ganin cewa ‘yan wasan ba wai ba sa kokari ba ne, kawai dai kwarewa suke bukata daga koci.

Amma yana da wahala Real Madrid ta kori Solari wanda ya tsawaita kwangilarsa zuwa 2021, yayin da ya rage wasa 12 a kammala La liga.

Makomarsa yanzu za ta dogara ne da rawar da zai taka a wasannin da suka rage a La liga.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...