Shekara 19 da Real Madrid ta bayyana Zidane dan kwallonta

Zidane Real Madrid

Hakkin mallakar hoto
Real Madrid FC

Ranar 9 ga watan Yulin 2001 Real Madrid ta bayyana Zinedine Zidane a matsayin dan wasanta, wanda ya taka rawa a matakin dan kwallo da koci.

Shekara 19 kenan da shugaban Real Madrid, Florentino Pérez da kuma Alfredo Di Stéfano suka gabatar da shi dauke da riga mai lamba biyar.

A matsayin dan wasa Zidane ya buga wa Real tamaula tsakanin 2001 zuwa 2006 ya kuma ci kwallo 49 a wasa 227 da ya buga mata.

Cikin kwallayen da ya ci ba za a manta da wacce ya yi kwance-kwance ya shimfida a raga ba a gasar Champions League a karawa da Bayer Leverkusen da suka yi a Glasgow.

Zidane ya lashe Champions League da Intercontinental Cup da European Super Cup da na LaLiga da kuma Spanish Super Cup biyu a matakinsa na dan kwallo.

A matsayinsa na koci, Zidane ya lashe Champions League uku da kofin La Liga da Club World Cup biyu da European Super Cup biyu da Spanish Super Cup biyu.

Zidane ya fara horar da karamar Real Madrid mai suna Castilla a 2014 zuwa 2016 daga nan ya karbi jan ragamar babbar kungiya a 2016 zuwa 2018 sai ya yi ritaya.

Dan kasar Faransa ya sake karbar jan ragamar Real Madrid a 2019 kawo yanzu.

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da tazarar maki daya tsakaninta da Barcelona ta biyu waccce ta yi wasa 35.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Deportivo Alaves ranar Juma’a a wasan mako na 35 a gasar ta La Liga.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...