Shafin YouTube ya janyo wa wani daurin shekara 4

An kama Muhammed Sekkaki da laifin yin kalaman batanci ga sarki Muhammad VI, da kiran 'yan kasar jakai

An yanke wa fitaccen mai wallafa bidiyo a shafin YouTube dan Morocco hukuncin zaman kaso na shekara 4 da tarar dala 4,000, bayan an same shi da yin kalaman batanci ga sarkin kasar.

A farkon wannan watan ne aka kama Muhammed Sekkaki sakamakon sukar Sarki Muhammad a wani jawabi da ya yi, tare da kiran ‘yan Morocco da jakai.

Sai dai ya na shirin daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa.

A wani hukuncin na daban, an daure dan jarida kuma mai fafutuka Omar Radi kan laifin wallafa sakon Twitter da ya zagi wani alkali a watan Afirilu da ya wuce.

Lauyansa ya ce za a ci gaba da tsare shi har sai ranar biyu ga watan Janairu inda za a gurfanar da shi gaban shari’a.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama a Morocco sun nuna damuwarsu kan yadda ake matsa wa mutane, musamman idan sun fadi albarkacin bakinsu kan wani abu da ya shafi masu mulkin kasar.

Tun bayan kadawar guguwar sauyi a yankin gabas ta tsakiya a shekarar 2011, Sarki Muhammad VI, ya raba madafun iko tsakanin fadarsa da zababbiyar gwamnatin kasar.

Sai dai masu sharhi kan al’amura na cewa har yanzu yana da karfin fada aji da zartar da hukunci na karshe a kan muhimman batutuwa a kasar.

More News

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Sojojin sun kama tarin makamai a a hannun mayakan IPOB

Rundunar sojan Najeriya ta samu nasarar kama makamai da suka hada bindigogi hodar hada bam a jihar. Rundunar ta samu gagarumin wannan nasara ne biyo...

Atiku ya ziyarci mahaifiyar su Yar’adua

Mai neman takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP, tsoshon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci mahaifiyar tsohon shugaban kasa, Umar Musa Yar'adua...