Serie A: Ibrahimovic ya koma AC Milan | BBC news

Zlatan Ibrahimovic

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ibrahimovic ya taba buga wa AC Milan wasa na shekara biyu

Tsohon dan wasan gaban kasar Sweden da Manchester United Zlatan Ibrahimovic ya koma AC Milan ta Serie A bisa yarjejeniyar wata shida tare da zabin karin shekara.

Dan wasan mai shekara 38 ba shi da kulob bayan ya bar kungiyar LA Galaxy ta kasar Amurka a karshen kakar wasa ta gasar Major League Soccer (MLS) ta bana.

Kungiyar AC Milan ta ce Ibrahimovic “zai isa birnin Milan domin gwada lafiyarsa rana 2 ga watan Janairu” sannan ya hade da abokan wasansa.

“Zan koma kulob din da nake girmaamawa da kuma garin Milan da nake kauna,” Ibrahimovic ya fada.
Ya buga wa AC Milan wasanni na shekara biyu daga 2010 zuwa 2012 – ya ci kwallo 42 a wasa 61 na Serie A.

Ya koma LA Galaxy ta kasar Amurka a watan Maris na 2018, inda ya ci kwallo 53 sannan kuma ya shiga cikin tawagar gasar MLS ta shekarun 2018 da 2019.

AC Milan ba ta kara daukar wani kofin kirki ba tun daga shekarar 2011 da ta dauki Serie A a karo na 18.

Tsofaffin zakarun Turai har sau bakwai, Milan suna fama a kakar bana yayin da suke matsayi na 11 a teburin Serie A da maki 21 a wasa 17.

Kungiyar ta kori kocinta Marco Giampaolo a watan Oktoba amma har yanzu ba ta sauya zani ba a karkashin Stefano Pioli.

Sun sha kashi a wasnsu na makon da ya gabata da ci 5-0 a hannun Atalanta, wanda rabon da hakan ta faru tun shekara 21.

More News

Kotu Ta Hana PDP Cire Shugaban RiÆ™on Jam’iyar

Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta hana jam'iyar PDP dakatar da Umar Damagum daga matsayinsa na shugaban riƙon jam'iyar. Mai Shari'a  Peter Lifu shi...

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...