
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce yan Najeriya na cikin jimami da alhini bayan mutuwar sarauniya Elizabeth.
Marigayiya sarauniyar ta mutu ne a ranar Alhamis tana da shekaru 96 a duniya.
A ranar Asabar ne shugaban ƙasar ya kai ziyarar ta’aziya ga Catriona Laing jakadar Birtaniya a Najeriya.
A yayin ziyarar ta’aziyar Buhari ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha wanda ya gana da Laing a Abuja
Mustapha ya rattaba hannu a rijistar ta’aziya a madadin shugaban kasa Buhari.
Sakataren na gwamnatin tarayya ya ce Najeriya da kuma yan Najeriya na alhini da jimamin mutuwar sarauniya mafi dadewa akan mulki a tarihin masarautar Birtaniya.