Connect with us

Hausa

Saraki ya fita daga APC

Published

on

 

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki ya bayyana ficewarsa daga jam’iyya mai mulki a kasar, APC.

Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter ranar Talata.

“Ina sanar da ‘yan Najeriya cewa bayan tattaunawa, na yanke shawarar fita daga jam’iyyar APC,” in ji shi.

Sai dai kawo yanzu Sarakin bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba tukunna. Kuma jam’iyyar APC ba ta mayar da martani ba kan batun.

Hakazalika Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed shi ma ya bayyana fitarsa daga jam’iyyar, sai dai shi ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar adawa ta PDP.

Saraki da Gwamna Abdulfatah wadanda tsofaffin ‘yan jam’iyyar PDP ne, sun koma jam’iyyar APC ne a shekarar 2014.

A makon jiya ne Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom shi ma ya sanar da ficewarsa daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa jam’iyyar PDP.

A farkon watan ne Kotun Kolin kasar ta wanke Saraki kan zargin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Wadanda suka fice daga APC a kwanan nan

Jam’iyyar APC ta kauce hanya – Buba Galadima
 • Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom
 • ‘Yan majalisar dokoki ta kasa 52 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP
 • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa’i
 • Suna dai samun goyon bayan Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi
 • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 – wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam’iyyar
 • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa – kamar yadda Daily Trust ta rawaito
 • Hakeem Baba Ahmed – shugaban ma’aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
 • Usman Bawa – mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.
Facebook Comments

Hausa

An samu Netanyahu da almundahana

Published

on

Benjamin Netanyahu

Image caption

Netanyahu ya ce ba zai yi murabus daga mukaminsa ba

Atoni janar na Isra’ila ya samu Firai Minista Benjamin Netanyahu da laifin cin hanci da rashawa da kuma laifin cin amana kan tuhume-tuhume uku da ake masa.

Ana zargin Netanyahu da karbar kyaututtuka daga hamshakan ‘yan kasuwa da alfarma.

Ya dai musanta aikata ba dai-dai ba tare da cewa bi-ta-da-kulli jam’iyyar adawa ke masa da ‘yan jarida.

Netanyahu ya kafe ba zai yi murabus daga mukaminsa ba, kuma babu dokar da ta ce ya yi hakan.

 • Netanyahu ya gaza kafa gwamnati, yanzu damar ta Gantz ce
 • Netanyahu: Ana gab da kammala bincike kan zargin cin hanci

Sai dai sanarwar samun shi da laifin rashawar na zuwa ne yayin da kasar ke shirin tsayawa cik na kwanaki biyu sakamakon karasa zaben da ba su kammalu ba, a zaben gama gari na watan Satumba da ya wuce.

A ranar Laraba, abokin hamayyar Netanyahu wato Benny Gantz ya sanar da har yanzu ya gagara samun rinjaye a majalisa da zai ba shi damar kafa gwamnatin hadaka.

Shugaba Reuven Rivlin ya bai wa Netanyahu damar samar da gwamnatin hadaka, amma har yanzu ya gagara hakan.

A ranar Alhamis shugaba Rivlin ya bukaci ‘yan majalisa su amince da firai ministan nan da makwanni uku, don gudun sake yin zabe karo na uku cikin shekara guda.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Me ya sa kwanaki hudu babu internet a Iran? | BBC news

Published

on

Iran
Image caption

Rashin internet ya shafi rayuwar ‘yan kasar, musamman matasa

Kasashen duniya sun fara nuna damuwa kan daukewar internet a kasar Iran, a dai-dai lokacin da aka shiga kwanaki hudu da daukewar.

Wannan ya biyo bayan zanga-zangar da ‘yan kasar ke yi kan Karin farshin man fetur da kasha 50, wanda gwamnatin shugaba Hassan Rouhani ta yyana.

A daren Asabar ne internet din ta fara fuskantar tangarda, kafin wayewar garin Lahadi ta dauke baki daya.

Iraniyawa mazauna kasashen ketare sun yi ta wallafwa a shafukan sada zumunta cewa daukewar internet ta raba su da ‘yan uwa da abokan arziki da ke gida lamarin da ya sanya ba su san a halin da suke ciki ba.

 • An kashe masu zanga-zanga 106 a Iran – Kungiyar Amnesty
 • Iran ta ‘samu rijiya mai gangar danyen mai biliyan 53’

Abin ya matukar tayar da hankali a kasar mai al’umma miliyan 80 da yawancin matasa sun dogara da internet dan gudanar da rayuwar yau da kullum ciki har da karatu.

Ba kamar sauran kasashen waje ba kamar Birtaniya da suke da kamfanonin sadarwa da internet daban-daban ba, wanda da wuya su iya daukewa a lokaci guda.

Iran na da kamfanoni biyu kwarara da kuma suke karkashin gwamnati, dan haka ne abin ya yi matukar tasiri.

Wata matashiya Arash Azizah ta wallafa a shafinta na Twitter yadda lamarin ya shafe ta;

”Kamar sauran Iraniyawa, muna da dandalin Whatsapp da zuriyar gidanmu ke amfani da shi, kakarmu a duk asubahin Allah ta na tura mana sakon fatan alkhairi da kariya daga dukkan abin ki, amma wannan matsala da aka samu ta hana mu yin hakan.”

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

An damke tsohon minista Adoke a Dubai

Published

on

Adoke

Hukumar ‘yan sandan kasa da kasa watau Interpol ta damke tsohon ministan shari’ar Najeriya bisa zargi sa da hannu a wata badakalar cin hanci kan danyen mai na fiye da dala biliyan daya.

Lauyan Mr Mohammed Bello Adoke ya tabbatar da tsare tsohon ministan a Dubai, amma ya ce bisa wani sammaci ne da lokacinsa ya wuce.

A baya Mr Adoke ya ce bai ci komai ba game da wata yarjejeniyar sayar da wata rijiyar mai a shekara ta 2011.

A cikin watan Afrilu ne hukumar yaki da rashawa a Najeriya – EFCC ta ba da sammacin kama shi tare da tsohon ministan man kasar, Dan Etete da kuma wani manaja a kamfanin mai na Italiya mai suna Eni.

Lamarin ya janyo shari’a mai tsawo tsakanin gwamnatin Najeriya da wasu kusoshi a kamfanonin mai na Eni da kuma Shell.

Sai dai duk kamfanonin biyu sun musanta aikata ba dai-dai ba.

Facebook Comments
Continue Reading

Trending

© Copyright 2019 - AREWANG Media Limited