Rundunar yan sanda ta musalta zargin yin garkuwa da yan sanda 10

0

Kwamishinan yan sandan jihar Kogi, Edward Egbuka ya musalta labaran dake yawo a gari cewa yansanda 10 ake zargin yan bindiga sun yi garkuwa da su lokacin da suke dawowa daga aikin zabe a jihar Osun.

Ya ce rundunar ta gano dukkanin yan sandan inda ya tabbatar da cewa yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocinsu a ranar Lahadi amma babu wanda suka yi garkuwa da shi.

Ya kara da cewa dukkanin yan sandan sun tsere cikin daji da aka kai musu harin saboda gudun kada ayi garkuwa da su.

Ya ce da kura ta lafa dukkanin yansandan da ake zargin an sace sun fito daga maboyar su inda suka hadu da abokan aikinsu a jihar Nasarawa.

Yan sandan na kan hanyarsu ne ta zuwa jihar Nasarawa lokacin da lamarin ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here