Rikicin Zamfara ya fi karfin jami’an tsaro kadai, inji Marafa

Sanata Kabiru Marafa

Hakkin mallakar hoto
ORDER PAPER

Image caption

Sanata Kabiru Marafa na jihar Zamfara ya bayyana cewa jami’an tsaron Najeriya kadai ba za su iya magance matsalar tsaron da ta addabi jiharsa ba.

A wata hira da BBC sanatan, ya ce saboda yadda matsalar da ‘yan bindiga ke satar shanu da kashe jama’a da kuma sace mutane domin karbar kudin fansa, ta yi muni dole jami’an tsaro na bukatar tallafin jama’a.

Sanatan ya ce duk wanda zai bayar da labarin halin da mutanen Zamfara suke ciki, kama da shi kansa, ba zai kai ga halin da jama’ar ke ciki ba, idan mutum ba ya je da kansa ya gani ba.

Ya ce kusan kashi 75 cikin dari na mazaje a jihar ba sa kwana a dakunansu idan dare ya yi.

Ya ce: ”Duk lokacin da aka ce maka Magariba ta yi an gama Magariba an gama sallar Isha’i, abin da kawai namiji zai yi shi ne ya je ya dauki dan balatinshi ko ‘yar gariyonshi ko danko ko wani abu, ya fita wasu su haye itace wasu su shiga wasu gine-gine suna gadin garuruwansu.”

Ya bayyana yin hakan da cewa ba wai yana nufin mutane sun dawo daga rakiyar jami’an tsaro ba ne, illa dai jami’an tsaron ba su da yawan da za a ce sun iya samar da tsaro gaba daya a ko ina, saboda haka akwai bukatar su ma kansu jama’a su tashi tsaye domin bayar da tasu gudummawar wajen kare dukiya da rayukansu.

Amma kuma ya ce babu shakka jami’an tsaro sun kasa tsare dukiya da lafiyar jama’a, kila saboda rashin yawansu ko rashin isassu.

A ranar Laraba Alhaji Kabiru Marafa ya gabatar da wani kuduri a majalisar dattawan Najeriyar, kan sha’anin tsaron jihar tasa ta Zamfara.

A kudurin ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti na musamman kamar wanda aka kafa a Arewa maso gabashin kasar, domin taimaka wa jama’ar da matsalar tsaron ta daidaita.

Ya ce jihar Zamfara tana cikin wani mummunan hali, na kama daga mata da aka kashe mazajensu da marayu kusan dubu 50, banda mata da aka yi wa fyade da kuma wasu da ke hannun barayi masu neman kudin fansa.

Ya ce kamata ya yi a cikin kasafin kudin wannan shekarar a ware kamar Naira biliyan 10 da za a ba wa wannan hukuma da ya ce a kafa, domin su kula da marayun da mata da aka kashe musu maza da sauransu.

Dan majalisar dattawan ya yi gargadin cewa muddin ba a yi haka ba, to matsalar ta Zamara, aba ce da za ta iya hade dukkan shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya gaba daya.

Sai dai a nata bangaren gwamnatin Najeriya ta ce an samu ci-gaba sosai a yakin da dakarun kasar suka daura da masu garkuwa da mutane a jihar ta Zamfara da sauran jihohin da ke makwabataka da ita.

Kakakin shugaban kasar, Mallam garba Shehu ne ya bayyana haka a wata hira da BBC.

Garba Shehu ya fadi hakan ne bayan da a ranar Laraba Majalisar Dattawan kasar ta zartar da wani kudiri, wanda ya bukaci gwamnatin tarayyar ta fito da wani tsari na shekaru goma don tallafa wa al’ummomin da suka jikkata a tsawon shekara biyar da aka shafe ana kashe-kashe a jihar ta Zamfara.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...