Rikicin Masarautar Kano: Abun Da Ya Faru A Zaman Kotu Na Yau Talata

A ranar Talata ne wata babbar kotun jihar Kano, ta dage ci gaba da zamanta har zuwa ranar 4 ga watan Yuli, domin ci gaba da sauraren kararar da aka shigar gabanta kan rikicin masarautar Kano.

Babban Lauyan Jihar Kano, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano da Majalisar Dokokin Jihar Kano, sune suka shigar da karar ta hannun lauyansu Ibrahim Isah-Wangida Esq, a ranar 27 ga watan Mayu, 2024.

Masu karar suna neman kotun ne ta haramta wa sarkin na 15, Aminu Ado-Bayero da wasu sarakuna hudu da aka tube daga sarautar Bichi, Rano, Gaya da Karaye da su daina bayyana kan su a matsayin sarakuna.

Sauran wadanda ake karar sun hadar da Sufeto-Janar na ’Yan sanda, Daraktan Hukumar DSS, Civil Defense da Rundunar Sojojin Najeriya.

A lokacin da ta zauna a yau domin sauraren shari’ar , Lauyan wadanda suka shigar da kara, Mista Eyitayo Fatogun SAN, ya shaida wa kotun cewa a jiya litinin 1 ga watan Yuli da misalin karfe 6:30 na yamma wanda ake kara na farko ya bashi takardar bayanansu.

“Ya mai shari’a sai a jiya da yamma muka ga takardar jawabai guda biyar kuma mun gabatar da dukkan martaninmu.

“Muna roko ga kotu da ta ba mu hutun mintuna 30 don ba mu damar yi wa wanda ake kara martanin mu.”

Lauyan Aminu Ado-Bayero, Abdul Muhammed SAN, ya soki rokon na basu mintuna 30, inda ya nemi a dage shari’ar domin ya ba shi amsa tare da shigar da dukkan bukatunsu.

Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu, ta dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 4 ga watan Yuli, domin sauraren duk wata bukata da ta fito daga kararrakin.

An rawaito cewa a ranar 27 ga watan Mayu ne kotun ta bayar da umarnin dakatar da wadanda ake kara na 1, 2, 3, 4 da Kuma 5 daga gabatar da kansu a matsayin sarakuna domin samun zaman lafiya a Kano.

Majalisar dokokin jihar a ranar 23 ga watan Mayu ta rusa dukkan sabbin masarautu hudu da aka kafa a jihar sannan Gwamna Abba Kabir-Yusuf, ya sake nada Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

More from this stream

Recomended