An samu gobara a rijiyar man fetur ta Akaso 4 da ke karkashin kamfanin man fetur na Najeriya mai lamba 18 Operating Limited a jihar Ribas.
Hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da kakakinta, Olaide Shonola, ta fitar a ranar Asabar.
Lamarin, wanda ya tsawaita a gefen kogin da ke makwabtaka da shi, an ruwaito cewa ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 11:12 na dare.
“NNPC 18 Operating Limited ta tabbatar da cewa an tura tawaga don ba da agajin gaggawa domin tabbatar da tsaron rijiyar, da magance lamarin tare da ware yankin da abin ya shafa ta hanyar amfani da kayayyakin da ke hana malala domin hana ci gaba da yaduwa da gurbacewar muhalli. Suna kuma shirin fara aikin kalato man nan take,” in ji Shonola.
Ta kara da cewa kamfanin ya tura jirgin ruwa na Naval House a yankin da lamarin ya faru tare da sa ido.
Yayin da take bayyana cewa har yanzu ba a san musabbabin faruwar lamarin ba, Shonola ta bayyana cewa ana shirin gudanar da bincike na hadin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki domin sanin musabbabin lamarin.