Rigakafin Malaria: Abubuwan da suka kamata ku sani kan riga-kafin cutar maleriya

A Health Surveilance Assistant gives a dose of the Malaria Vaccinne into the first recipient on April 23, 2019 at Mitundu Community hospital in Malawi's capital district of Lilongwe
Bayanan hoto,
Kananan yara a kasar Malawi, cikin wannan hoton, har ma da kasashen Ghana da Kenya na cikin wannan shiri kasha na farko

Kasancewar akwai kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar fiye da 260,000 da ke mutuwa daga cutar ta maleriya a kowace shekara a yankin Kudu da Saharar Afirka, wannan ci gaba da aka samu zai ceci dubun-dubatar rayuka, WHO ta bayyana.

Amma yaushe ne mutane za su fara amfana daga wannan ruwan rigakafin da ake kira RTS,S?

Za mu duba wannan da kuma sauran wasu muhimman tambayoyi.

Masu bincike da kwararru a kan harkokin kiwon lafiya na nuna farincikinsu bayan da Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO ta amince da amfani da ruwan allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya na farko a fadin duniya.

Yaya tasiri da kuma kariyarsa ta ke?

Shekaru shida suka gabata ne aka tabbatar da sahihancin ruwan rigakafin, wajen bayar da kasha 40 bisa dari na kariya daga kamuwa da cutar maleriya da kuma kasha 30 bisa dari na cutar zazzabin mai tsanani.

Tun a shekarar 2019 ne masu bincike suka fara gudanar da shirin bayar da allurar rigakafin a kasashen Ghana, da Kenya da kuma Malawi.

Kananan yara fiye da 800,000 ne aka yi wa allurar rigakafin akalla sau daya, kuma WHO ta bayyana cewa babu wata damuwa game da batun hadari.

Babu wani abin damuwa don kariyar kadan ce

A bayyana ta ke cewa zai fi dacewa idan ya fi yawa, amma abinda da mutane da zama za su ce shi ne akwai bukatar yin tunani game da girman matsalar – idan aka duba miliyoyin daruruwan kamuwa da cutar, raguwar kasha 40 bisa dari har yanzu gagarumin adadi ne na yawan rayukan aka ceto.

“Wannan ruwan rigakafi ne mai matsakaicin inganci … [Amma] ceto, da bayar da kariya, da kaucewa kashi 30 zuwa 40 bisa dari na yawan adadin kamuwa da cutar zai haifar da gagarumin amfani ga al’umma,” jami’in hukumar WHO Pedro Alonso ya shaida wa BBC.

Mahukunta a bangaren kiwon lafiya su ma sun jaddada cewa wannan sabon makamin ne a yakin da ake yi da cutar zazzabin cizon sauron ko kuma maleriya da za a yi amfani da shi tare da sauran matakan kariya, kamar su gidan sauraon da aka jika da ruwan sinadarai da kuma magungun kashe kwayoyin cutar ta maleriya.

Ta yaya rigakafin zai yi ke aiki?

Maleriya kwayar cuta ce da ke shiga tare da yi wa kwayoyin halittar jininmu lahani don kara hayayyafa, kuma tana yaduwa ne daga cizon saurayen da ke zukar jinni.

Ruwan rigakafin na kai farmaki kan kwayar cutar mai hadari da aka fi samu a Afirka: Plasmodium falciparum.

Ya kan yi kokari wajen yi wa kwayoyin cutar lahani jim kadan bayan shigarsu cikin jinin wanda sauraon ya ciza, ta hanyar toshe duk wasu kafofin shiga cikin kwayoyin halittar dan adama na wucin gadi, don haka zai bayar da kariya daga kamuwa da cutar, kamar yadda Dakta Alonso ya bayyana.

Ana bukatar yin rigakafin sau hudu don yin tasiri. Ana bayar da guda ukun farko wata daya tsakanin kowanne daga watanni biyar, da shida da kuma bakwai, kana ana bukatar bayar da na karshen a watanni 18.

Kananan yara ne aka bayyana da wadanda suka fi kasancewa cikin hadarin mutuwa daga kamuwa da cutar ta zazzabin cizon sauro, ba kamar manya ba wadanda ke da damar sake inganta garkuwar jikinsu.

Nawa za a kashe kana su wanenen za su biya?

Kamfanin harhada magunguna mafi girma GSK ne ya hada ruwan rigakafin, ya kuma yi alwashin samar da su a kan farashin kamfani na kashi 5 bisa dari amma bai bayyana takamaimen farashin ba.

Idan aka zo batun sayen shi, yanzu ya ragewa kasashe da masu bayar da tallafi su fitar da kudade.

“Yanzu dole sai kwamitin bayar da tallafi na kasa da kasa ya tattauna kana ya yanke shawarar yadda za a sayi ruwan rigakafin,” jagoran kamfanin na GSK Thomas Breuer ya shaida wa BBC.

Rose Jalang’o, wacce ke taimaka wa wajen tsara kashin farko na shirin bayar da allurar rigakafin a kasar Kenya ta bayyana cewa mahukunta na jiran shawarwari daga kasashen duniya kan yadda za a sayi ruwan rigakafin a wani bangare na shirin bayar da rigakafi na kasa baki daya.

Yanzu haka a kasar ta Kenya, akasarin taimakon kudaden alluran rigakafi na zuwa ne daga masu bayar da tallafi irin su gamayyar kungiyar samar da rigakafi ta duniya Gavi da kuma gidauniyar Bill and Melinda Gates.

Wadanne lokuta ne aka tsara na rarrabawa?

Za a cigaba da farko na shirin bayar da rigakafin a kasashen Ghana, da Kenya da kuma Malawi.

Kamfanin na GSK ya bayyana cewa ya bayar da gudumawar ruwan allurar rigakafin miliyan 10 na yin binciken kuma yanzu haka an yi amfani da rubu’i daga ciki.

GSK din ya kuma yi alwashin samar da ruwan rigakafi miliay 15 a ko wace shekara. Idan aka samu kudaden daga nan za a fara samun shi a wadace don amfani a kasashe da dama daga karshen shekarar 2022 ko kuma farkon shekarar 2023, kamar yadda Mista Breuer ya bayyana.

Amma wannan adadi ba lallai ya wadatar ba. Zuwa karashen shekaru goman mai yiwuwa za a bukaci akalla ruwan rigakafin kusan miliyan 100 a ko wace shekara, kamar yadda Ashley Birkett daga kungiyar Path, wacce ta taimaka wajen tsara shirin bayar da rigakafin ta bayyana.

Wadanne irin kayyakin aiki ko gine-gine ake bukata?

Kasancewar ruwan rigakafin an kirkiro shi ne da bufin yi wa kananan yara ‘yan kasa da shekara biyu, za a iya hada shi da sauran shirye-shiryen bayar da allurar rigakafin da aka saba yi wa kananan yara, don haka ba a bukatar karin wasu gine-gine ko na aiki.

Haka kuma, ba a bukatar wani shirin wayar da kan jama’a da horar da ma’aikatan kiwon lafiya.

A kashin farko na shirnin a kasar Kenya, an yi wa kananan yara 200,000 rigakafin kuma an samar da shi a kauyuka da wurare masu nisa ta hanyar shirin kai wa ga dimbin jama’a da dakunan shan magani masu nisa, Dakta Jalang’o ta shaida wa BBC.

Wadanne sauran rigakafi ne aka ake kokarin kirkirowa?

Ana gudanar da aiki kan sauran ruwan rigakafin, da suka hada daga Jami’ar Oxford a Birtaniya. A cikin watan Aprilu, masu bincike sun bayar da rahoto kan gwajin farko tare da yin nuni da cewa yana da ingancin kashi 77 bisa dari.

Amma hada ruwan rigakafin maleriya na daukar tsawon lokaci saboda cut ace mafi sarkakiya wajen shawo kai fiye da cutar korona misali.

RTS, S shi ne ruwan rigakafin cutar maleriya na farko da aka taba yi wa binciken kwakwaf da gwaje-gwaje, amma WHO ta bayyana cewa ruwan rigakafin cutar maleriya da biyu ”ka iya kasancewa mafi amfani wajen shawo kan cutar” saboda zai taimaka wajen biyan bukatun da dama.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...