Rashin Karfafawa Jami’an Tsaron Najeriya Shi Ke Kawo Koma Baya a Fannin Tsaro

Wannan yana zuwa ne lokacin da ‘yan ta’adda ke ta samun galaba suna kashe jami’an tsaro da aka samar domin kare rayukan jama’a.

Daya daga cikin yunkurin da gwamnatin Najeriya ke yi wajen ganin an shawo kan matsalar rashin tsaro, shi ne tura jami’an tsaro a duk wuraren da aka samu rahoton samun ayyukan ta’addanci.

Sai dai duk da samar da jami’an tsaron hakan ba ya hana ‘yan ta’addar ci gaba da gudanar da ayyukansu, yawancin lokuta ma su kan yi fito-na-fito da jami’an tsaron, inda ake samun asarar rayuka daga bangarorin biyu.

A kudancin Najeriya ma ana ta samun rahotannin cewa ‘yan bindiga sun hallaka jami’an tsaro a jihohi daban daban.

Hakan na faruwa ne lokacin da al’umomi ke kokawa akan cewa jami’an da aka tura yankunansu sun yi kadan musamman bisa la’akkari da yadda ‘yan bindiga ke zuwa da yawa idan za su yi aika-aikar su.

Wannan lamarin a cewar mai sharhi akan lamurran tsaro Captain Yahaya J. Umar mai ritaya yana faruwa ne saboda gwamnati taki kula wajen karfafa hukumomin tsaro.

Ita dai gwamnatin Najeriya na cewa tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta karfafawa hukumomin tsaronta ta hanyar sayo kayayyakin aiki.

Ganin cewa gwamnati ta na ta daukar matakai wadanda har yanzu za’a iya cewa sun kasa samar da biyan bukata, watakila da za ta jarraba wasu shawarwari na masana a samu biyan bukata.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

Ɗan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...