Rashin aikin yi da talauci shi ya haifar da Boko Haram—OBJ

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce a farkon rikicin Boko Haram a yankin Arewa-maso-Gabas, wadanda suka kafa kungiyar ta’addancin sun shaida masa cewa talauci da rashin aikin yi ne ya jefa su cikin wannan aika-aika.

Sai dai ya yi gargadin cewa sama da yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a kasar nan za su iya zama ‘yan Boko Haram nan gaba idan ba a gaggauta magance su ba.

Ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da wani littafi mai suna, ‘Pillars of Statecraft: Nation-building in a change world’ wanda ‘yarsa, Dokta Kofo Obasanjo-Blackshire ta rubuta a wani taron da aka yi a Legas.

Da yake amsa tambayar daya daga cikin mahalarta taron kan dalilin da ya sa manufofin gwamnati suka zama siyasa fiye da na mutane a ‘yan kwanakin nan, ya ce wani bangare na manyan matsalolin kasar nan shi ne a kullum ana neman wanda za a daura wa alhakin matsalolinta ne.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...