Rashford zai tsawaita zamansa a United

Marcus Rashford

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Manchester United ta fara zaman tattaunawa da Marcus Rashford game da tsawaita yarjejeniyarsa a Manchester United.

Rashford, mai shekara 21, wanda Louis van Gaal ya bai wa dama a United ya taka rawar gani a jagorancin Jose Mourinho ya kuma dora kokarinsa a karkashin Ole Gunnar Solsjaer.

Dan wasan tawagar Ingila ya ci kwallo na 10 a bana a fafatawar da United ta yi nasara a kan Leicester City 1-0 a ranar Lahadi, kuma shi ne na biyu matashi da ya ci kwallo 100 a United, bayan Ryan Giggs.

A kakar badi ne kwantiragin Rashford zai kare a Old Trafford, amma da yarjejeniyar za a iya tsawaita zamansa zuwa karshen kakar 2021.

United wadda ta tsawaita zaman Anthony Martial zuwa kakar 2024, tana tattaunawa da David De Gea domin ya ci gaba da zama a Old Trafford.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...