Ranar Asabar ce Sallar Idi a jamhuriyar Nijar

Issoufou

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Majalisar Malaman addinin Musulunci da ke jamhuriyar Nijar ta ce ranar Asabar ne Sallah karama a jamhuriyar bayan ganin jaririn wata a garuruwa biyar a fadin kasar.

Wata sanarwa da Majlaisar ta fitar ta ce an ga jariirn watan na Shawwal a birnin Magaria da ke cikin jihar Damagaram wato Zinder da kuma a garuruwan Maine-Soroa da N’guiguimi da N’Gourti da ke cikin jihar Diffa mai iyaka da jihar Borno a Najeriya.

Haka ma jinjirin watan Shawwwal ya samu fita a garin Oungoudague da ke cikin yankin Tsibirin Gobir dake gundumar Gidan Rounji a jihar Maradin Katsina.

Majalisar ta ce ranar Asabar ne 1 ga watan Shawwal. Hakan na nufin al’ummar jamhuriyar Nijar sun yi azumi 29.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Saudiyya ta bayar da sanarwar yin Sallar Idi ranar Lahadi.

More from this stream

Recomended