Peter Cech ya buge fenariti a kwallon Hockey

Peter Cech

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tsohon wanda ya tsare ragar Chelsea da Arsenal, Peter Cech ya buge fenatiti biyu a wasan farko da ya buga wa kungiyar kwallon Hockey, Guildford Phonix.

Guildford ta buga gasar kwallon Hockey da Swindon Wildcats 2.

Mai shekara 37, wanda ke aiki a Chelsea ya tare fenaritin farko da ta karshe, inda aka zabe shi wanda ya fi taka rawa a gasar.

Tun farko Phoenix ce ta ci 2-1 bayan zango biyu, sai dai daf da za a tashi ne Taylor Wootton ya farke, hakan ne ya sa ata je bugun fenariti.

Dan kasar Jamhuriyar Czech wanda ya dade yana sha’awar wasan ya samu wannan damar, bayan da ya dunga atisaye tukuru tun bayan da ya yi ritaya daga taka-leda.

Cech mai shekara 37 ya ce yana fatan zai bai wa matasan ‘yan wasa gudunmawa domin bunkasa kungiyar.

Tun lokacin da Cech ya koma Ingila da taka leda a 2004 a Chelsea ya rungumi kungiyar kwallon Hockey ta kankara Guildford Phoenix a matsayin wadda yake goyon baya.

Cech wanda ya yi wa Jamhuriyar Czech wasa 124 ya lashe kofin Premier hudu da na FA Cup biyar da League Cup uku da Champions League da na Europa a murza leda da ya yi a Ingila.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...