Osibanjo ya ziyarci wuraren da ambaliyar ruwa ta yi barna a jihar Anambra

A cigaba da ziyarar da yake kaiwa yankunan da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a kasarnan, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ziyarci jihar Anambra a yau ranar Alhamis.

Osinbajo ya kewa wuraren da ambaliyar ruwan ta yi mummunan barna.

Mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano da kuma ministan kwadago Chriss Ngige.

A lokacin da yake zagayawa wuraren a cikin kwale-kwale Osibanjo ya jajantawa mutanen da abin ya shafa inda ya ce gwamnatin tarayya za ta tallafa musu.

“A yau ina daya daga cikin wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Otuocha dake Anambra domin ganin halin da yan uwan mu mata da maza suke ciki abin akwai kada zuciya.Zamu samarwa wadanda abin ya shafa abinci da kuma kayan agaji.muna jajanta muku.”Osinbajo ya ce.

A farkon makon nan ne gwamnatin ta tarayya ta ayyana dokar ta baci kan ambaliyar ruwan bayan da mutane sama dari suka rasa rayukansu da kuma asarar dukiya ta biliyoyin naira.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...