Obasanjo ya koma matukin Adaidata Sahu

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya gudanar da haya da babur din Adaidata sahu inda ya rika daukar fasinja a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Obasanjo ya ce yayi haka ne domin ya nunawa matasa cewa akwai sana’oin da za su iya yi domin su samu kudi ta halastacciyar hanya.

Tsoshon shugaban kasar ya ce ya dauki matakin ne domin sake jaddada abin da ya fada a watan Nuwambar shekarar 2002 a yayin kaddamar da “Keke NAPEP” da gwamnatinsa ta samar domin matasa su zama masu dogaro da kai.

More from this stream

Recomended