NNPP Tayi Babban Kamu a Jigawa

Jam’iyar NNPP mai kayan marmari tayi babban kamu a jihar Jigawa bayan da wasu manyan yan siyasa suka sauya sheka ya zuwa jam’iyar daga APC.

Wasu bayanai da suka fito daga wata majiya mai tushe dake kusa da dantakarar gwamnan jihar a karkashin a NNPP, Alhaji Aminu Ibrahim su ne suka tabbatar da haka.

A cikin wadanda suka sauya shekar sun hada da Sanata Sabo Nakudu, Sanata Ahmed Mahmoud Gumel, Sani Jumbo da sauran manyan yan siyasa da dama.

More from this stream

Recomended