Bayan ganawar sa’o’i shida a ranar Litinin, gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyar kwadago bayan da gwamnati ta yi alkawarin cewa shugaba Bola Tinubu ya kuduri aniyar biyan mafi karancin albashi na sama da N60,000.
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ne ya sanar da hakan bayan kammala taron da shugabannin kungiyoyin kwadago suka yi a Abuja wanda aka fara da karfe 5 na yamma kuma aka kammala ‘yan mintoci zuwa karfe 11 na dare.
Ya ce shugaban kasar ya “yi alkawarin biyan mafi karancin albashi na kasa wanda ya haura N60,000”.
Rahotanni sun nuna cewa kungiyar kwadagon da ta kunshi kungiyar kwadago ta Najeriya da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta bayyana yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan ma’aikatan Najeriya albashi.