Nigeria @60: Waiwaye kan tarihin ƙabilar Ibo a Najeriya

Wannan maƙala ce ta musamman da BBC ta rubuta albarkacin murnar cikar Najeriya shekara 60 da samun ƴancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Burtaniya.

Za mu kawo tarihi na manyan ƙabilun ƙasar huɗu da suka haɗa da Hausawa da Yarabawa da Igbo kuma Fulani cikin kwana huɗu a jere.

Kamar sauran ƙabilun Najeriya, tarihin al’umar Ibo shi ma yana tattare da bayanai da zato da fahimta da ra’ayoyi iri daban-daban, har ma da jayayya a tsakanin masana tarihi, musamman ma game da asalin inda al’ummar ta Ibo ta samo tushenta, inda masana tarihi da dama suke ikirari cewa, al’ummar ta Ibo ta samo asalinta ne daga Isra’ila, don haka tana da dangantaka da Yahudawa.

Kuma daga can ne Ibon suka fito, har suka iso wajen da suka samu mazauni na dindindin a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Sai dai kuma fahimta da amannar Farfesa Ihechukwu Madubuike, wani malamin jami’a, tsohon ministan ilimi a Najeriya, kuma yanzu haka shi ne shugaban cibiyar farfado da harshen Ibo da al’adunsa ta Jami’ar Gregory, da ke garin Uturu na jihar Abiya, sun sha bamban.

”Bayani mafi makama, wanda na fi amanna da shi, mu mazauna ne na asalin na musamman a wani waje da ake kira Ugwuele, kusa da garuruwan Uturu da Okigwe.

”Ba wai daga wani wuri daban muka yi ƙaura muka zo yankin kudu maso gabashin Najeriya ba”.

”Duk wasu hasashe-hasashe da sauran ruwayoyin da ake riƙo da su a tarihance, cewa ‘yan ƙabilar Ibo ko kuma wasu daga cikin Ibon sun fito ne daga Isra’ila da sauran wurare makamantan haka, har yanzu zato ne kawai ake bayyanawa.

”Tartibin bayani mafi makama dai, shi ne al’ummar Ibo ba ta fito daga ko’ina ba”.

Al’adu

Ita ma al’ummar Ibo tana da nata al’adu da kuma addinin da take bin kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, a cewar Farfesa Ihechukwu Madubuike:

”Al’adar al’umma ita ce, illahirin al’amuransu, wadda ta ƙunshi abubuwan da sukan yi yau da kullum, da yadda cimarsu take, da yadda suke noma, da yadda suke raye-rayensu, da yadda suke magana, da yadda suke kallon duniya da dai sauransu”.

”Addinin gargajiya na dan kabilar Ibo, shi ne bauta wa Ubangiji guda daya, wanda muke kira ‘Chukwu’, wanda ke nufin Ubangiji mai girma.

”Abin da ke nuna cewa akwai wasu ƙananan ababen bauta na gargajiya, waɗanda a kan bi ta wajensu a kai ga ‘Chukwu’ ko ‘Chineke’, wanda shi mahaliccin dukkan halittu. Sai daga baya ne Turawan mulkin mallaka suka shigo mana da addinin Kirista.”

Al’ummar Ibo dai sun yi fice a sana’o’i da harkokin kasuwanci, abin da Farfesa Ihechukwu Madubuike ya ce a jininsu yake.

”Ibo mutane ne masu matuƙar sauƙin cuɗanya da sauran al’ummomi, masu aiki tukuru ne. Kafin zuwan Turawa, babbar sana’ar Ibo ita ce noma.

”Ibo yana da kokarin samun wani abu daga inda ake ganin kamar babu komai. Wannan ya sa za ka ga akwai ‘yan kabilar Ibo a cikin harkokin kasuwanci da masana’antu da dai sauransu, kuma suna samun ci gaba”.

Yawan al’ummar Ibo wani abu ne da masanin tarihin ya ce, ya zuwa yanzu babu tartibiyar kididdiga game da shi, sai dai a yi kiyasi.

”Yawan al’ummar Ibo ya zarta miliyan hamsin a duniya baki daya, akwai Ibo ‘yan asalin wurare daban-daban a kusan kowacce jiha ta kudancin Najeriya.

”Muna da ire-iren wadannan Ibo a jihohi Akwa Ibom da Kuros Riba, da Ribas da Delta da Edo. Kuma sana’o’i da harkokin kasuwanci sun kai su sauran sassan kasar, da ma kasashen waje.

”Harshen ƙabilar Ibo na ɓacewa”

Kamar sauran harsunan Najeriya da dama, shi ma harshen Ibo yana fuskantar ɗumbin kalubale, a cewar Farfesa Ihechukwu Madubuike.

”Irin yadda jama’ar Ibo suke yawan amfani da harshen Turanci, hakika wani babban cikas ne. Wata matsalar kuma da muke fama da ita, ita ce babu malamai da yawa da ke koyar da wannan harshe a makarantu.

”A halin yanzu kuma wasu harsunan suna kokarin mamaye harshen Ibo. Amma dai muna kokarin bin hanyoyin da suka kamata, don shawo kn wannan matsala.”

Duk ta yadda aka kalli tarihin al’ummar dai, ja-in-ja da ake kansa abu ne da ake ci gaba da gudana tsakanin masana tarihi, kamar yadda abin ya ke game da tarihin sauran kabilun Najeriya da dama.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...