Neymar na tsaka mai wuya, Chelsea ta dage don dauko Chilwell | BBC Hausa

NEYMAR

Hakkin mallakar hoto
@neymarjr

Dole dan wasan Brazil Neymar, mai shekara 26, ya amince a rage kusan £26m daga albashinsa idan yana son komawa Barcelona daga Paris St-Germain a bazarar. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Babban abin da Paris St-Germain ta sanya a gaba yanzu shi ne sabunta kwantaragin dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 21, a bazara duk da rashin kudin da take fama da shi saboda annobar korona. (ESPN)

Chelsea na shirin kara kaimi a yunkurin da take yi na dauko dan wasan Leicester Ben Chilwell, mai shekara 23. (Sun)

Mamallakin Inter Miami David Beckham ya yi magana da Real Madrid a game da yiwuwar sayo dan wasan Colombia James Rodriguez, 28. (Goal)

Golan Liverpool Loris Karius, mai shekara 26, ya shirya komawa Wolves a matsayin aro a kakar wasa mai zuwa. (Fantatik – in Turkish)

Karius ya kusa soke zaman aron da yake yi na shekara biyu a Besiktas domin ya koma Anfield saboda matsalar da ya samu da kungiyar sakamakon rashin biyansa alawus-alawus dinsa. (Guardian)

  • Juventus za ta sayo Kane, Paris St-Germain za ta sabunta kwangilar Neymar
  • Ba zan sayar da Kane a Ingila ba – Levy

Sabbin masu sayen Newcastle sun mayar da hankali wurin dauko dan wasan Paris St-Germain dan kasar Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 33, sannan suna son nada Massimiliano Allegri ko Mauricio Pochettino a matsayin sabon kocin kungiyar. (ESPN)

Arsenal ta soma tattaunawa da Atletico Madrid a kan yarjejeniyar dauko dan kwallon Ghana Thomas Partey, mai shekara 26, a cewar mahaifin dan wasan. (Mail)

Tottenham na sha’awar sayo dan wasan Real Betis dan kasar Brazil Emerson, mai shekara 21, wanda kuma dan wasan Barcelona ne. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Kazalika Tottenham na shirin fafatawa da Inter Milan a kokarin dauko dan wasan Barcelona dan kasar Brazil, Arthur, mai shekara 23. Mundo Deportivo – in Spanish)

Chelsea tana gogayya da Atletico Madrid domin dauko dan wasan da ke buga gasar U21 a Netherlands Mohamed Sankoh, mai shekara 16, daga Stoke. (Goal)

Kungiyoyin Premier na duba yiwuwar komawa atisaye ranar 9 ga watan Mayu inda manajoji da dama suka shaida wa ‘yan wasansu cewa su shirya komawa fagen tamaula. (Sun)

Dan wasan Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Yannick Bolasie, mai shekara 30, zai koma Everton bayan Sporting Lisbon ta rage wa’adin zaman aron da yake yi a can da zummar yin tsimi. (A Bola – in Portuguese)

Kocin Schalke David Wagner ya ce kungiyar ba za ta iya sayen Jonjoe Kenny, mai shekara 23, daga Everton ba, amma za ta so tsawaita zaman aron da yake yi a can zuwa kakar wasa ta badi. (Sky Sports)

Leeds za ta dauko dan wasan Portugal Helder Costa, mai shekara 26, daga Wolves ranar 1 ga watan Yuli duk da matsalolin rashin kudi da ta fada a ciki sakamakon cutar korona. (Football Insider)

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

Ƴan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da suka yi bacci a lokacin da suke tsare da mutanen da suka sace

Jami'an Æ´an sanda sun samu nasarar kama wasu masu garkuwa da mutane bayan da suka buge da sharar bacci a lokacin da suke tsare...

Gwamnatin Adamawa Ta Ƙara Hutun Ɗaliban Makarantu Saboda Annobar Cutar Ƙyanda

Gwamnatin jihar Adamawa ta tsawaita lokacin komawar É—aliban jihar makarantunsu domin fara  zangon karatu na uku saboda annobar cutar Æ™yanda. A wata sanarwa ranar Litinin,...

Sojan Jamhuriyar Nijar sun kama Gawurtaccen ÆŠan Fashin dajin Najeriya Kachalla Mai Daji

Dakarun sojan Jamhuriyar Nijar sun samu nasara kama gawurtaccen É—an fashin dajin nan mai suna Kachalla Mai Daji a garin Illela dake kan iyakar...