NDLEA ta kama wata da ake zargi da safarar hodar Iblis zuwa Pakistan

Hukumar NDLEA da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi Najriya, ta ce ta cafke wata mata ‘yar kasuwa da ake zargi da da hada kai da wasu ‘yan kasar Pakistan wajen safarar hodar iblis zuwa Lahore, babban birnin Pakistan.

Matar mai suna Okefun Darling Chisom, ta shiga hannun jami’an na NDLEA ne a filin tashi da saukar jirage na Legas da ke kudancin Najeriya.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar dauke da sa hannun Daraktan yada labarai, Femi Babafemi, ta ce an kama Chisom da hodar iblis da nauyinta ya kai kilo 8.

NDLEA ta ce Chisom ta boye hodar iblis din ce a cikin na’urar amsa kuwwa, yayin da take kokarin hawa jirgin kamfanin Qatar Airways zuwa Lahore inda za ta ratsa ta Doha a ranar Asabar 5 ga watan Nuwamba.

Bincike ya nuna cewa matar ta na da alaka da wasu ‘yan Pakistan biyu da suka hada da Asif Muhammad mai shekaru 45 da Hussain Naveed mai shekaru 57

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...