NDLEA ta kama hodar ibilis ta sama da biliyan 194

0

Hukumar NDLEA dake sha da fataucin miyagun kwayoyi ta samu nasarar kama hodar ibilis da kudinta ya kai sama da biliyan 194 a jihar Lagos.

Wannan ne kamen hodar ibilis mafi girma a tarihin hukumar ta NDLEA.

Jami’an hukumar sun kama hodar ne a wani dakin ajiye kayayyaki dake Ikorodu a jihar ta Lagos.

A wata sanarwa da kakakin hukumar Femi Baba Femi ya fitar ya ce hukumar ta shafe shekaru da dama tana bibiyar ayyukan mutanen.

A cikin mutanen da aka kama akwai dan kasar Jamaica daya da kuma yan Najeriya hudu.