Najeriya za ta karbo ‘ya’yan mayakan kungiyar IS

Mayakan IS

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Najeriya za ta kasance kasar farko da ta karbi yara marayu masu alaka da mayakan kungiyar ‘yan ta-da-kayar-baya ta IS a Afirka.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa wani jami’i ne ya karbi wadannan yara daga hannun mahukuntan Kurdawa a madadin gwamnatin Nijeriya.

Yaran kuma sun hadar da mace daya da namiji biyu, wadanda shekarunsu suka kama daga biyar zuwa 10.

Kuma an ambato shi jami’in na cewa gwamnatin Nijeriya tana bibiyar k’arin wasu batutuwa na irin wadannan yara, da ke hannun Kurdawa.

Mai magana da yawun gwamnatin Nijeriya Mallam Garba Shehu ya shaida wa BBC halin da ake ciki.

Jami’in mai suna Musa Habib ya ce sun bukaci ma’aikatar hulda da kasashen wajen Kurdawa ta ba su jerin sunayen yaran da mahaifansu suka fito daga Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka da ke hannunta.

Malam Garba Shehu, ya ce gwamnatin kasar na ci gaba da tuntubar ofishin jakadancin Nijeriya da ke Lebanon don samun tabbaci ko yaran uku, ‘ya’yan dan Nijeriyan nan da aka yi zargin cewa ya je Siriya don yaki a karkashin kungiyar ‘yan ta-da-kayar-bayan IS, Ibrahim Uwais.

Hatta a lokacin da mayakan Kurdawa ke yaki da sauran ‘yan ta-da-kayar-bayan da suka shiga fadan sari-ka-nok’e, akwai dubban mayak’an IS da iyalansu da ke tsare a hannunsu.

Daga ciki kuma daruruwan mayakan da ake zargi ‘yan kasashen waje ne wadanda ke tsare a gidajen yari, da kuma dubban iyalansu da ke cunkushe a sansanoni.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mata da kananan yara ne suka fi shan wuya a duk lokacin da ake yaki

Kasashen Yamma da dama dai na nuna kin amincewa su karbi mutanen kasashensu.

Amma Jamus da Faransa da Beljiyum sun karbi kalilan daga cikin irin wadannan marayu inda suka mayar da su gida.

Ko a bara ma sai da Amurka ta karbi wata mata da ‘ya’yanta hudu da suka fito daga kasar.

Haka zalika kasashen Kazakhstan da Uzbekistan da Kosovo su ma tuni sun mayar da gomman mata da kananan yara ‘yan kasashensu zuwa gida.

Mayakan Kurdawa dai su ne suka jagoranci yak’i da kungiyar IS da goyon bayan Amurka a Siriya.

A watan Maris din wannan shekara ne suka fatattaki ‘yan ta-da-kayar-bayan daga wani yankin na karshe da suke rik’e da shi a wannan kasa da yak’i ya daidaita.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...