
Hukumar NAFDAC dake kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya ta bankado wasu wurare da ake yin kayan sha da na ci na bogi.
Hukumar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce ta kai samamen ne a garin Aba dake jihar Abia.
Shugabar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce biyo bayan sirri da suka samu hukumar ta gano cewa an dauki lokaci mai tsawo mutanen suna aikata wannan mummunan aiki.
Sai dai biyo bayan sanarwar ne yan Najeriya da dama suka shiga bayyana ra’ayinsu inda suka nuna cewa sakacin hukumar ne ya janyo ake irin wannan aikin.
