NAFDAC ta ce kar ƴan Najeriya su riƙa cin abincin da ya wuce kwana 3 a firij

Darakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, ta bukaci ‘yan Najeriya da su guji ajiye dafaffen abinci a cikin firiji sama da kwanaki uku.

Adeyeye ta yi gargadin cewa dafaffen abincin da ake ajiyewa a cikin firij na kwanaki yana da saurin kamuwa da sinadarai masu haddasa cututtuka.

Adeyeye ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Talata mai dauke da sa hannun mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na hukumar, Sayo Akintola.

Adeyeye, wadda ya bayyana hakan a yayin bikin ranar kiyaye abinci ta duniya na 2024 ta bukaci masu ruwa da tsaki a harkar samar da abinci da su dauki matakan da suka dace don kafa al’adun kare abinci a cikin ayyukansu na rage hadarin abinci da kasadar da ka iya yin illa ga lafiyar abinci.

Majalisar Dinkin Duniya ta kafa ranar kiyaye abinci ta duniya da ake yi kowace shekara a ranar 7 ga watan Yuni a shekara ta 2018 don wayar da kan jama’a da karfafa yunƙurin hanawa, ganowa da magance haɗarin lafiyar jama’a da ke da alaƙa da abinci mara kyau.

More from this stream

Recomended