Mutum sama da 80 sun mutu a rikicin makiyaya da manoma na Filato

A wani mummunan rikicin da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a jihar Filato, akalla mutane 85 ne suka mutu yayin da sama da mutane 3,000 suka rasa matsugunansu, kamar yadda rahotanni suka bayyana a ranar Alhamis.

Mutane 30 ne suka mutu lokacin da rikici ya barke a ranar Alhamis a kauyuka daban-daban na jihar Filato.

Rikicin kabilanci da addini ya dade yana shafar yankin.

A cewar wasu majiyoyi da shaidun gani da ido, rikicin ya ci gaba da faruwa, kuma a ranar Alhamis din da ta gabata, al’ummar kauyuka da dama a yankin Mangu da ke Jihar Filato na ci gaba da fama da shi, inda wasu kuma suka tsere daga gidajensu.

Wasu dalilai da ba a tantance su ba ne suka haddasa hare-haren da aka kai a Mangu a wannan makon, amma kashe-kashen da ake yi tsakanin manoma da makiyaya akai-akai ya kai wani mataki.

Kawo yanzu dai an gano gawarwakin mutane 85 a cewar Mista Daput Daniel, shugaban karamar hukumar.

More News

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...