Mutanen Mazaɓar Sanata Abdul Ningi Sun Nemi Kotu Ta Soke Dakatarwar Da Aka Yi Masa

Mutanen da suka fito daga mazaɓar dakataccen dan majalisar dattawa,  Sanata Abdul Ningi sun shigar da ƙara a gaban babban kotun tarayya dake Abuja inda suka nemi kotun da ta soke dakatarwar da aka yi masa.

Wasu daga cikin mutanen mazaɓar ne suka shigar da ƙarar a ranar Laraba  masu shigar da ƙara da suka haɗa da Sadiq Abubakar, Abdullahi Jibrin, Adamu Hassan, Shafiu Abdullahi, Magaji Shafihu, William John, Yahaya Saleh, Yusuf Adamu, Adamu Sulaiman, da kuma  Habibu Mamuda sun fito ne daga mazaɓar Dan Majalisar Dattawa Ta Bauchi Ta Tsakiya.

Suna  ƙarar Majalisar Dattawan Najeriya, shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio, Sanata Olamilekan Adeola, akawun majalisar ƙasa, akawun majalisar dattawa da kuma dogarin majalisar.

A cikin ƙarar lauyan masu ƙara, Rueben Egwuaba ya ce mutanen mazaɓar na buƙatar kotun ta bayar da umarnin mayar da Abdul Ningi muƙaminsa na Sanata mai wakiltar mazaɓar Bauchi Ta Tsakiya tare da dukkanin hakki da damarmaki dake tattare da muƙamin nasa.

Sun kuma buƙaci kotun ta hana waɗanda ake ƙara yin duk wani abu da zai hana mai ƙara gudanar da aikinsa na ɗan majalisar dattawa.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...