Mutane biyar sun mutu sanadiyar fashewar bututun mai a jihar Imo

Rundunar yan sandan jihar Imo ta ce mutanen da basu gaza biyar ne ba suka mutu sakamakon fashewar bututun mai a garin Obiti dake karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar.

Henry Okoye mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce lamarin ya faru ne ranar Talata inda ya ɗora alhakin fashewar kan ɓarayin ɗanyen mai.

Okoye ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, Aboki Danjuma ya kafa wata tawaga domin su gano musabbabin faruwar lamarin tare da kamo masu laifin da suka tsere.

“Fashewar ya faru ne ranar Talata kuma kusan mutane biyar ne suka mutu. Sun ƙone ƙurmus a yanzu muna gudanar da bincike tare haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro domin gano ko suwaye suke wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa,”Okoye ya ce.

“Sun je fasa bututun mai ne kamar yadda suka saba lokacin da abun ya faru.”

More from this stream

Recomended